MAGANIN
SANYIN MATA KO INFECTION
Idan mace tana fama da kaikayi ko
kuraje ko fitar farin ruwa mai wari ko bushewa ko daukewa ko budewa da kwailewa
da rashin sha'awa ko gamsuwa da sauran cututtukan sanyi, sai a gwada daya daga
cikin wadannan hanyoyi.
1)A samu Saiwar Garafuni da
Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da
shi. Kullum sau daya. Yana maganin budewa da kaikayi.
2) A samu Garafuni da Sassaken
Sanya sai a tafasa, Sai mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Yana
fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.
3) A samu Furen Tumfafiya, sai a
shanya ya bushe, a daka a dinga Zubawa a cikin Nono ana sha. Yana magance
matsalar ruwan infection.
.
4) A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.
.
4) A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.
5) A samu Kabewa a dafa ta, bayan
an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono
sannan a sa Zuma a sha.
Wannan yana mganin rashin sha'awa da bushewa da rashin gamsuwa.
Wannan yana mganin rashin sha'awa da bushewa da rashin gamsuwa.
6) A dafa Zogale, idan ya dahu sai
a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi. Yana maganin fitar
farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma yana kara ni'ima.
7) A samu `Dan-Tamburawa da
Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki. Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga
shigarta. Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna. Zai magance mata
kaikayi da kuraje kuma yana sa matsewa.
8) A samu Farar Albasa da Kanumfari
da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi, sai ta dake su tayi Yaji ta
dinga cin abinci da shi. Yana saukar da ni'ima da magance duk matasalolin
sanyi.
9) A samu Sabulun Zaitun da
Sabulun Habba sai a daka su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a
tankade. Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwa6a da Ma'ul Khal, a
zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum
sau daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu yana maganin
kuraje da kaikayi da fitar wari.
10) A samu Man Zaitun da Man Habba
da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hadesu waje daya. Mace ta dinga shan
cokali daya kullum kafin ta karya. Yana wanke dattin mara kuma yana samar da
ni'ima.
No comments:
Post a Comment