ABUBUWAN DA SUKE KAWOWA MATA CIWON SANYI KO
INFECTION.
1)Rashin sanya pant.
2)Barin pant yayi dauda sosai ba a canja ba.
Ana so in da hali kullum a canja pant sau biyu a wanke.
3)Saka pant a jiqe da ruwa.
4)Yawan tsarki da ruwan sanyi.
5)Yawan tsarki da ruwan da zafinsa yayi yawa.
6)Rashin aski.
7)Wasa da gaba.
8)Yawan cin `Danyar Albasa.
9)Yin amfani da Magungunan mata marasa
inganci.
10)Dadewa akan Masai ko toilet.
11)Rashin shan iska.
12)Musanyar tufafi.
13)Saduwa da mai cutar.
12)Cutar Aljanu, wato Jinnul Ashiq. Su ma
suna sanyawa mace infection mai wuyar magani.
-------------
ILLOLIN DA SANYI KO INFECTION YAKE YI WA MATA
1)Yana sa Rashin Sha'awa.
2)Yana sa ciwon mara mai tsanani.
3)Yana haifar da kurajen bakin mahaifa ko ya
toshe mahaifar baki daya.
4)Yana sa mace ta dinga jinin al'ada baki
kirin mai wari.
5) Yana sanya farin ruwa mai wari ya dinga
fito mata.
6)Yana sanyawa a dinga jin mace tana wari
mara dadi kuma a rasa ta ina yake fitowa duk wankanta.
7)Yana sa jin zafi yayin saduwar aure ko kuma
ganin jini a maimakon ruwa.
8)Yana rikitawa mace kwanakin al'adarta, su
dinga karuwa ko raguwa ko jinin ya dinga wasa.
9)Yana sanyawa mace tusar gaba, wato iska ta
dinga fita ta gabanta.
10)Yana sanyawa mace yawan `Barin ciki ko
kuma rashin shigar cikin kwata-kwata.
11)In yayi karfi yana hana mace haihuwa.
12) Wani infection din alama ce ta zaman
Aljanu a jikin mace, musamman idan tana mafarkin namiji dare ko jarirai.
Abin lura:-
Idan mace tayi magungunan Asibiti
da kuma irin wadannan da mu ka ambata amma infection din bai warke ba,
To ta nemi maganin jinnul Ashiq, wato magungunan Aljanu don zai iya yiwuwa
matsalarsu ce.
arkin Fada-Matsalolin Ciwon Sanyin-Mata
(Sanyin-Gaba) [Vaginitis/Toilet infection], Rigakafi da Magani.
---
‘Sanyi’ kalma ce mai fadin ma'ana da Malam Bahaushe ke yin amfani da ita domin
yin kokarin bayanan wasu matsalolin lafiya na daban-daban , misali ,
ciwon-sanyin jiki [rheumatism], ciwon sanyin mura [ cold and flu] da kuma ciwon
sanyin-mata [Vaginitis] ko ciwon sanyin maza-da-mata da ake samu ta hanyar
jima'i [STDs like chlamydia, gonorrhea, syphilis, genital herpes, HPV etc] da
sauransu. Saidai Malam Bahaushe baya kiran ciwon sida/kanjamau [HIV/AIDS] da
ciwon-sanyi duk da cewa kau anfi yada cutar ta jima'i.
Za muyi bayani akan ciwon sanyin-mata ne
kadai [Vaginitis]. Matsalolin ciwon sanyin-mata [vaginitis/vaginal infections
or toilet infections] wasu cututuka ne ko matsaloli dake addabar gaban mace,
wato cututtuka masu sanya kaikayin farji, ko radadin ciwo, kumburin gaba ko
warin gaba , zubar farin ruwa, kurajen farji, zafi wajen yin fitsari ko wajen
yin jima'i da sauransu. Ciwon sanyin-wata matsala ce dake faruwa ga mata da
dama a cikin wasu lokutta na rayuwarsu. Ana samun wannan cututtuka ko matsaloli
sabili da wani sauyin yanayin jiki da mata ke samu wasu lokutta da kuma sabili
da wasu kwayoyin halittar 'bacteria' da 'fungus' dake zaune cikin al'aurar
mace, haka kuma , mata na iya samun wannan ciwon a lokacin juna-biyu da kuma
shayarwa [during pregnancy and breastfeeding] . Har ila yau, za'a iya samun
ciwon ta hanyar jima'i [vaginal intercouse] da wasu dalilan ko hanyoyi na
daban.
Nau'in ciwukan sanyin-mata suna da yawa, to
amma bincike ya nuna cewa ciwon sanyin-mata nau'i uku ne (3) suka fi addabar
mata da yawa. Za muyi bayani akansu kadai, a takaice insha Allahu, sune kamar
haka: (sunayen su da yaren turanci) 1. 'Yeast infection' 2. 'Bacterial
vaginosis' 3. 'Trichomonas'
1. ‘Yeast infection’ ('Candidiasis'). Akwai
wasu kwayoyin halittun 'fungas' (masu suna 'candida') sune ke haddasa 'Yeat
infection'. Su wadannan halittu wanda kwayar idon mutum baza ta iya ganin suba
, saboda kankaantar su saida taimakon madubin likita ne za'a iya ganin su
[microscope] . Halittun suna rayuwa a wasu wurare cikin jikin mutum kuma
adadinsu baya da yawa . Ana samunsu cikin farji kuma, asali basu cika cutarwa
ba.'Candida' suna san wuri mai gumi, lema da rashin iska domin girma da yaduwa.
Idan suka samu wannan yanayi da suke so toh za suyi yawa su kuma haddasa ciwon
sanyin 'Yeast infection'. Anfi yawan samun irin wannan ciwon sanyi ga mata da
yawa , kusan kashi 75 cikin 100 na mata sun taba samun wannan ciwon a cikin
wasu lokutta na rayuwarsu. Alamomin cutar sun hada da: zubar farin ruwa mai
kauri daga farji, kuraje ko kaikayin farji da kuma labban farji suyi jawur ko
cikin farji.
2. ‘Bacterial vaginosis’ , cuta ce dake
shafar farji sabili da girman wasu kwayoyin halittun 'bacteria' masu cutarwa
dake cikin farji suna rayuwa. Alamonin cutar sun hada da: zubar ruwa mai
'karnin kifi daga farji, warin sa musamman lokacin jima'i, ko radadin zafi
lokacin fitsari, amma babu kaiyayi cikin alamomin. Alamomin cutar kuma na iya
'buya.
3. ‘Trichomoniasis ’ : A cikin cututtukan
sanyi da muka yi bayanin su a baya (wato cuta ta 1 da ta 2) , 'Trichomoniasis'
ta 3, itace cutar sanyin-mata da ake yadawa ta hanyar jima'i ga maza (STD) fiye
da sauran a zahiri, wato mace zata iya harbin mijinta da cutar ko mijin ga
matar. Idan ya kasance miji nada wata mata ko yana neman matan waje masu cutar
ko kuma macen ta taba saduwa da wani mutum mai cutar daya samo cutar daga wata
mace, to akwai yiwuwar ma'aurata su samu cutar koma mafi hadari HIV da wasu
cututtukan jima'i (STDs). Ana kiran 'yar kankanuwar halittar [parasitic
organism] dake sanya wannan cuta da suna 'Trichomonas vaginalis'. Mazaje ba
kaso suke sanin suna da cutar ba kasancewar alamomin cutar basu cika bayyana ga
maza ba. Yawanci sai idan ciwon ya kama matan su suna cikin neman magani suke
gano suna da cutar. Idan anyi sa'a alamomin ciwon sun bayyana ga maza, ana iya
samun alamomi kamar haka: zubar farin-ruwa kadan, zafi kadan bayan fitsari ko
bayan fitar maniyyi. Alamomin cutar ga mata suna iya kama da ciwon sanyi na 1
da na 2 da muka yi bayani a sama, ko kuma: zubar ruwa mai launin kore-da-dorawa
- mai kumfa da wari, zafi wajen yin fitsari, rashin jin dadi wajen jima'i.
Wannan cuta tana da hadari ga mace mai juna-biyu ga abunda ke cikinta, musamman
idan ba'a nemi magani ba.
Matakin da Zaki Dauka Idan Har Kinga Alamomin
Ciwon-Sanyi
Idan har kina da daya ko biyu daga cikin wadannan alamomin ciwon kai koma fiye
da haka, mataki na farko da zaki dauka shine, ki garzaya zuwa asibiti ko wata
cibiyar lafiya domin neman taimako. A asibiti ne idan anga kwararriyar likita,
musamman 'gynaecologists' wanda suka shahara akan fagen matsalolin mata , za'a
duba matsalar, sa'annan ayi bincike 'lab test' ko da 'microscope' asan abunda
ke damun ki a kuma baki maganin daya dace da shawarwari. Haka kuma , idan anyi
binciken kuma an tabbatar da irin ciwon sanyin dake damun marar lafiyar toh
za'a iya zuwa wannan cibiya tamu mai albarka ta Madinah Islamic Medicine
Katsina domin neman magani/waraka da yardar Allah.
Wasu Halayen Da Zasu Iya Taimakawa Wajen Samun Ciwon Sanyi da Rigakafin su:
> Wajen Tsaftace Gaba [ Vaginal Douching]
A cikin farji akwai wasu kwayoyin halittar 'bacteria' marar sa cutarwa kuma
masu amfani (wato 'Normal flora'). Su 'normal flora' suna taimakawa wajen bada
kariya ga farji daga wasu nau'in 'bacteria' na daban masu cutarwa (masu suna
'Bacterial pathogens'). Garin neman kiba akan nemo rama, wasu mata kanyi amfani
da wasu hanyoyi domin tsaftace farji, kamar ta hanyar yin amfani da sabullan
magani, harba magani cikin gaba, ruwan dumi da gishiri ko dettol domin wanke
farji don tsaftacewa ko rigakafi daga 'bacteria' da zata iya cutarwa. Wadannan abubuwa
da ake amfani dasu don rigakafi na kashe 'bacteria' masu amfani [the normal
flora] cikin farji, hakan zaisa 'bacteria' masu cutarwa su samu damar shigowa
cikin farji su cutar da lafiya da ciwon-sanyi, sabili da babu 'bacteria' mai
bada kariya dake hana su shiga ko 'barna. Don haka , idan har lafiyar ki lau
kuma kina son tsaftace gabanki toh sai ayi amfani da ruwa , musamman lokacin
wanka a tsaftace gaba. Ki guji fesa turare ko wanke gaba da sabili mai kamshi.
Idan har lafiyar ki lau kada kiyi amfani da wani abu idan ba ruwa ba. Ki sani
cewa farji yana tsaftace kanshi da kanshi a yanayin halittarshi, yana fitar da
wani ruwa [secrets fluid] na musamman dake wanke illahirin gaban mace.
> Kayan-sawa na ciki/wandon pant
[Under-wears/under-pants] Wasu matan kanyi amfani da wandon pant ko
'skin-tight' kwana da kwanaki ba tare da canzawa ba ko wankewa. Irin wannan
halin kazanta na dauda da lema, na bawa cututtuka (Germs) dama su shiga cikin
farji su kuma girma cikin 'dan kankanin lokaci har su haddasa ciwon sanyi. Don
haka , yana da kyau a canza 'under-wears' wankakku masu tsafta a kowace rana.
Idan lokacin zafi ne ko kinyi aiki kuma akwai zufa a jikin ki to sai ki canza
wando akalla sau 2 a rana. Kuma yana da kyau ayi amfani da wandon da akayi da
auduga [cotton under-wears] domin yana taimakawa wajen tsotse lema da bushewa,
sabanin wando da akayi da 'nylon' [nylon under-wear].
> Wajen wanke bayan-gida [Way of cleaning
the anus after faeces] Yana daga cikin halayen wasu mata idan sunyi bahaya suna
fara wanke dubura sa'annan gabansu, wasu kuma suna hadawa ne duka , wato
gabansu da dubura su wanke lokaci daya, wannan ba dabi'a bace ba mai kyau ga
mace, domin kuwa idan kika wanke dubura farko sa'annan gabanki ko kika wanke su
a lokaci daya toh zaki iya goga ma farjinki wasu cututtuka dake cikin
kashi/bayan gida. Don haka , sai a fara wanke farji farko, bayan angama wanke
shi da ruwa da kyau to sai a wanke dubura.'Toilet infection' kalma ce da mutane
suka kirkira kuma ta samu asali ne daga mummunar dabi'ar wanke dubara tare da
farji, wanda wasu ke tunanin shine ke kawo cutar sanyin-mata. Toh saidai
dadilan dake kawo cutar sanyin mata suna da yawa kamar dai yanda mu kayi bayani
a baya, kuma ita kalmar 'Toilet infection' ba tada muhalli a cikin 'Kamus din
likitoci a matsayin sunan cuta. Mutane ne wanda ba ma'aikatan lafiya ba suke
amfani da kalmar da nufin 'vaginal infections' ko 'vaginitis' (kalmar da
ma'aikatan lafiya suka fi amfani da ita).
> Tsugunni a bandaki [Squatting in
toilets] Yin tsugunni a bandakin da mutane da yawa ke amfani dashi nada hadari
ga lafiya, musamman bandaki mai dauda da kazanta. Sau da yawa mace zata
tsugunna tayi fitsari cikin bandaki sai fitsarinta ya doki kasa yayi tsalle ya
fallatso mata ko ya dawo mata tare da wani ruwan dake kwance a kasa ko fitsarin
wata macen.Digo daya na fitsarin mai ciwon sanyi zai iya harbar ki da ciwon
idan ya fallatso maki ga ga gaba.Don haka, idan zaki yi fitsari kada kiyi inda
kowa keyin fitsari a cikin bandaki, ki samu wuri na daban mai tsafta cikin
bandakin kuma inda babu ruwa a kwance. Haka kuma kada ki bari gabanki ya taba
kasa. Kiyi fitsari a hankali. A yawaita wanke bandaki kullum da dettol ko
danginshi 'germicides' masu inganci domin kashe cututtuka.
> Yin amfani da wandon pant na 'kawar ki,
yar'uwar ki ko wata mace [Sharing under-wears] Kawar ki, kanwar ki ko wata
yar'uwarki mutane ne masu iya kamuwa da cuta. Zai iya kasancewa suna da
ciwon-sanyi , don haka idan kina jin cewa kinyarda da ita ko kuma kun zama jini
da tsoka toh ki shirya fama da ciwon sanyi da zasu iya harbarki dashi idan kina
amfani da wandon su. Koda basu da ciwon , bai kamata ku rinka amfani da pant
din junanku ba. Riga kafi yafi magani.
> Rashin kula wajen yin jima'i [Sexual
intercourse without care] Yanada matukar muhimmanci ki kiyaye da jin rauni a
farji a lokacin saduwa da maigida. Barin gashin gaba ba'a rage shiba da kuma
yin jima'i tsawon lokaci ko da karfin tsiya na daga cikin dalilan dake sa mace
ta samu rauni a gabanta. Samun rauni ko fashewar fata cikin al'aura na bawa
cututtuka kofar shiga jiki su cutar da lafiya da 'infections'.
>Mataki na biyu da zaki iya dauka shine:
bayan kin san abunda ke damun ki domin a asibiti an bayyana maki, idan har ya
tabbata sanyi ne kuma kin sha magani amma baki samu sauki ba, ko kuma kin samu
sauki amma baki warke duka ba yana dawowa, toh zaki iya amfani da wannan
taimakon da zamu baki :
Ki samu 'Khal tufah' [Apple cider vinegar] a Islamic Chemist. Ki tafasa ruwa
mai yawa yayi zafi, idan yayi 'dumi sai ki samu robar wanka ki juye ruwan ya
cika robar, sa'anna ki zuba khal tufah cikin ruwan kimanin adadin kofin shayi
[small tea cup] 1 ko 2 cikin robar wankan, sai ki zauna ciki minti 15. Bayan
kin tashi daga robar sai ki tsane lemar ruwan dake gabanki da tawul mai kyau ya
bushe. Sai ki samu man-kwakwa [coconut oil] da auduga ki goge gabanki,
man-kwakwa nada sinadarai masu kashe kwayoyin cuta [ antiviral, antibacterial
and antifungal properties] Kiyi amfani da man-kwakwa sau 3 a rana. Za kiyi
amfani da Khal tufah kamar yanda mu kayi bayani kullum sau 1 a rana har sai kin
samu sauki.
Haka kuma, zaki iya amfani da Tafarnuwa [Garlic]. Ki samu salar tafarnuwa 2 ko
1 ki karkare bawon da ledar ta, kiyi matsi dasu da dare idan zaki kwanta bacci
sai da safe ki cire ki yar. Tafarnuwa magani ce mai karfi (kuma 'antibiotic') ,
itama tana da sinadarai masu kashe cututtuka [antiviral, antibacterial and
antifungal properties]. Kuma zaki iya cin tafarnuwa ko amfani da 'capsules'
nata, idan zaki iya.
Bugu da kari, zaki iya neman garin Hulba
[Fenugreek powder] a Islamic Chemist da zuma (honey) kiyi shayi, ki tasa ruwa
ki zuba hulba karamin cokali 1 cikin kofin shayi ki motsa, sai ki sha. Kiyi
haka safe da dare, har sai kin samu sauki. Idan mace tana da juna-biyu kada
tayi haka sai ta nemi shawarar likitan Islamic Chemist/ likitan asibiti da
yasan 'Hulba' ko masani amma babu laifi ga mai shayarwa tayi amfani da hulba,
hakan zai kara samar mata da ruwan nono. Masu juna-biyu su guji sha-shayen
magunguna ba tare da izinin likita ba.
Allah ya taimaka.
Madinah Islamic Medicine: Wannan bayanai suka
gabata kokarin bincike ne da wallafar Hausa na Madinah Islamic, Katsina. Za'a
iya yima bayanan gyara a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Don neman karin
bayani ko gyara, ko kuma neman magungunan Musulunci akan matsalar da wasu sai a
kira +23484028794 ko email: madinahislamicmed@gmail.com